Menu

Zabura 123

BIB

1 Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama.

2 Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa.

3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa.

4 Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate