Menu

Zabura 122

BIB

1 Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.”

2 Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima.

3 An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda.

4 A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.

5 A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda.

6 Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

7 Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.”

8 Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”

9 Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate