Menu

Zabura 124

BIB

1 Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce,

2 da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana,

3 sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai;

4 da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.

5 Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.

6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.

7 Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira.

8 Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate