Menu

Zabura 121

BIB

1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo?

2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.

3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.

5 Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;

6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare.

7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka;

8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate