Menu

Zabura 20

BIB

1 Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.

2 Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.

3 Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela

4 Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.

5 Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.

6 Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa.

7 Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.

8 Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram.

9 Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate