Menu

Zabura 149

BIB

1 Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka.

2 Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.

3 Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.

4 Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.

5 Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.

6 Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,

7 don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane,

8 don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,

9 don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate