Menu

Zabura 150

BIB

1 Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.

3 Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo,

4 yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

5 yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate