Menu

Zabura 127

BIB

1 In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza.

2 Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.

3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi.

4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

5 Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate