Menu

Zabura 126

BIB

1 Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.

2 Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”

3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki.

4 Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb.

5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

6 Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate