Menu

Zabura 92

BIB

1 Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,

2 don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,

3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya.

4 Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.

5 Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai!

6 Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba,

7 cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada.

8 Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.

9 Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta.

10 Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina.

11 Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.

12 Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon;

13 da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.

14 Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,

15 suna shela cewa, “Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate