Menu

Zabura 87

BIB

1 Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.

2 Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.

3 Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, Sela

4 “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ”

5 Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”

6 Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” Sela

7 Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate