Menu

Zabura 82

BIB

1 Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.

2 “Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela

3 Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

5 “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.

6 “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.

7 Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”

8 Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate