Menu

Zabura 8

BIB

1 Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.

2 Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

3 Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,

4 wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?

5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

7 dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji,

8 tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.

9 Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate