Menu

Zabura 75

BIB

1 Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.

2 Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci; ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.

3 Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza, ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela

4 Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.

5 Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”

6 Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.

7 Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.

8 A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas.

9 Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,

10 wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate