Menu

Zabura 67

BIB

1 Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela

2 don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.

3 Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.

4 Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela

5 Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.

6 Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.

7 Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate