Menu

Zabura 61

BIB

1 Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.

2 Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.

3 Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.

4 Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela

5 Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.

6 Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.

7 Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.

8 Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate