Menu

Zabura 6

BIB

1 Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.

2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.

3 Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?

4 Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.

5 Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari?

6 Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye.

7 Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.

8 Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.

9 Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata.

10 Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate