Menu

Zabura 3

BIB

1 Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!

2 Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela

3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

5 Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

7 Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye.

8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate