Menu

Zabura 130

BIB

1 Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

2 Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai.

3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya?

4 Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka.

5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

6 Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.

7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.

8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate