Menu

Zabura 13

BIB

1 Har yaushe, ya Ubangiji? Za ka manta da ni har abada ne? Har yaushe za ka ɓoye fuskarka daga gare ni?

2 Har yaushe zan yi kokawa da tunanina kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata? Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina?

3 Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna. Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa;

4 abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,” kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi.

5 Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa; zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.

6 Zan rera ga Ubangiji gama ya yi mini alheri.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate