Menu

Ayuba 25

BIB

1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

2 “Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa; yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.

3 Za a iya ƙirga rundunarsa? A kan wane ne ba ya haska haskensa?

4 Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?

5 In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa,

6 mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate